Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu |
| 2 |
| Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo. |
| 3 |
| Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu. |
| 4 |
| Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki. |
| 5 |
| Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa, |
| 6 |
| wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi, |
| 7 |
| wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai. |
| 8 |
| Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki. |
| 9 |
| Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara. |
| 10 |
| Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. |
| 11 |
| Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba. |
| 12 |
| Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna. |
| 13 |
| Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/065.mp3
150
65