Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, |
| 2 |
| don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. |
| 3 |
| Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka. |
| 4 |
| Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. |
| 5 |
| Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. |
| 6 |
| Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu. |
| 7 |
| Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/067.mp3
150
67