Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa. |
| 2 |
| Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah. |
| 3 |
| Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki. |
| 4 |
| Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa. |
| 5 |
| Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki. |
| 6 |
| Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana. |
| 7 |
| Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, |
| 8 |
| duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila. |
| 9 |
| Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji. |
| 10 |
| Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta. |
| 11 |
| Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa, |
| 12 |
| “Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima. |
| 13 |
| Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.” |
| 14 |
| Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon. |
| 15 |
| Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne. |
| 16 |
| Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada? |
| 17 |
| Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa. |
| 18 |
| Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can. |
| 19 |
| Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. |
| 20 |
| Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa. |
| 21 |
| Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa. |
| 22 |
| Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku, |
| 23 |
| don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.” |
| 24 |
| Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki. |
| 25 |
| A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna. |
| 26 |
| Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila. |
| 27 |
| Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali. |
| 28 |
| Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā. |
| 29 |
| Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai. |
| 30 |
| Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi. |
| 31 |
| Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah. |
| 32 |
| Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, |
| 33 |
| gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya. |
| 34 |
| Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari. |
| 35 |
| Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah! |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/068.mp3
150
68