Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka, Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata, |
| 2 |
| Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni, Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni, A can za su yayyage ni kamar zaki. |
| 3 |
| Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan, Wato idan na yi wa wani laifi, |
| 4 |
| Idan na ci amanar abokina, Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili, |
| 5 |
| To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni, Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni, Su bar ni ƙasa, matacce! |
| 6 |
| Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji, Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana! Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi. |
| 7 |
| Ka tattaro dukan kabilun da suke kewaye da kai, Ka yi mulki a kansu daga Sama. |
| 8 |
| Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane. Ka shara'anta mini bisa ga adalcina, Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki. |
| 9 |
| Ka tsai da muguntar mugaye, Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki. Kai Allah mai adalci ne, Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu. |
| 10 |
| Allah ne mai kiyaye ni, Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya. |
| 11 |
| Allah alƙali ne mai adalci, Kullum kuwa yana kā da mugaye. |
| 12 |
| Idan mutane ba su tuba ba, Allah zai wasa takobinsa, |
| 13 |
| Zai ɗana bakansa ya shirya shi, Zai ɗauki makamansa masu dafi, Ya kuma auna kibansa masu wuta. |
| 14 |
| Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa, Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi. |
| 15 |
| Yana haƙa rami mai zurfi a ƙasa, Sa'an nan yă fāɗa ramin da ya haƙa! |
| 16 |
| Saboda haka muguntarsa ta hukunta shi ke nan, Rikicin kansa ya yi masa lahani. |
| 17 |
| Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa, Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/007.mp3
150
7