Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na, |
| 2 |
| in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba. |
| 3 |
| Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana, |
| 4 |
| in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana, |
| 5 |
| to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. |
| 6 |
| Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci. |
| 7 |
| Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa; |
| 8 |
| bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka. |
| 9 |
| Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya. |
| 10 |
| Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya. |
| 11 |
| Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana. |
| 12 |
| In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa. |
| 13 |
| Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta. |
| 14 |
| Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya. |
| 15 |
| Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa. |
| 16 |
| Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa. |
| 17 |
| Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/007.mp3
150
7