|
| 1 |
|
| A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya. |
|
| 2 |
|
| Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni. |
|
| 3 |
|
| Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata. |
|
| 4 |
|
| Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta. |
|
| 5 |
|
| Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro. |
|
| 6 |
|
| Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka. |
|
| 7 |
|
| Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi. |
|
| 8 |
|
| Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini. |
|
| 9 |
|
| Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare. |
|
| 10 |
|
| Gama abokan gābana suna magana a kaina; waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare. |
|
| 11 |
|
| Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.” |
|
| 12 |
|
| Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni. |
|
| 13 |
|
| Bari masu zagina su hallaka da kunya; bari waɗanda suke so su cutar da ni su sha ba’a da kuma kunya. |
|
| 14 |
|
| Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau. |
|
| 15 |
|
| Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba. |
|
| 16 |
|
| Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai. |
|
| 17 |
|
| Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki. |
|
| 18 |
|
| Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa. |
|
| 19 |
|
| Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah? |
|
| 20 |
|
| Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni. |
|
| 21 |
|
| Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni. |
|
| 22 |
|
| Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila. |
|
| 23 |
|
| Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa. |
|
| 24 |
|
| Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice. |
|
|
|
|