|
| 1 |
|
| Hakika, Allah yana yi wa Isra'ila alheri, Da waɗanda suke da tsarkin zuciya! |
|
| 2 |
|
| Amma ina gab da fāɗuwa, Ƙafafuna sun kusa zamewa, |
|
| 3 |
|
| Saboda na ji kishin masu girmankai, Sa'ad da na ga mugaye suna arziki. |
|
| 4 |
|
| Ba su jin zafin ciwo, Su ƙarfafa ne, lafiyayyu. |
|
| 5 |
|
| Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha, Ba su da wahala kamar sauran mutane, |
|
| 6 |
|
| Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya, Suka sa hargitsi kuma kamar riga. |
|
| 7 |
|
| Zuciyarsu, cike take da mugunta, Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle. |
|
| 8 |
|
| Sukan yi wa waɗansu ba'a, Suna faɗar mugayen abubuwa, Masu girmankai ne su, suna shawara A kan yadda za su zalunci waɗansu. |
|
| 9 |
|
| Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama, Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya, |
|
| 10 |
|
| Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu, Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu. |
|
| 11 |
|
| Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba, Maɗaukaki ba zai bincika ba!” |
|
| 12 |
|
| Haka mugaye suke. Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi. |
|
| 13 |
|
| Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki, Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi? |
|
| 14 |
|
| Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini, Kana horona kowace safiya! |
|
| 15 |
|
| Da na faɗi waɗannan abubuwa, Da na zama marar gaskiya ga jama'arka. |
|
| 16 |
|
| Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan, Ko da yake ya cika wuya, |
|
| 17 |
|
| Sai sa'ad da na shiga Haikalinka, Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye. |
|
| 18 |
|
| Hakika ka sa su a wurare masu santsi, Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai! |
|
| 19 |
|
| Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su, Suka yi mummunan ƙarshe! |
|
| 20 |
|
| Ya Ubangiji, kamar mafarki suke Wanda akan manta da shi da safe, Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa. |
|
| 21 |
|
| Sa'ad da zuciyata ta ɓaci, Hankalina ya tashi, |
|
| 22 |
|
| Sai na zama wawa, ban fahimta ba, Na nuna halin dabba a gabanka. |
|
| 23 |
|
| Duk da haka ina tare da kai kullayaumin, Kana riƙe da hannuna. |
|
| 24 |
|
| Shawararka, tana bi da ni, Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja. |
|
| 25 |
|
| In banda kai, wa nake da shi a Sama? Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya? |
|
| 26 |
|
| Kwanyata da jikina za su raunana, Amma Allah ne ƙarfina, Shi nake so har abada! |
|
| 27 |
|
| Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu, Za ka hallakar da marasa aminci gare ka. |
|
| 28 |
|
| Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah! Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah, Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata. |
|
|
|
|