|
| 1 |
|
| Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya. |
|
| 2 |
|
| Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa. |
|
| 3 |
|
| Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi. |
|
| 4 |
|
| Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi. |
|
| 5 |
|
| Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam. |
|
| 6 |
|
| Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga. |
|
| 7 |
|
| Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka. |
|
| 8 |
|
| Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya. |
|
| 9 |
|
| Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya. |
|
| 10 |
|
| Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace. |
|
| 11 |
|
| Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?” |
|
| 12 |
|
| Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa. |
|
| 13 |
|
| Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi. |
|
| 14 |
|
| Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya. |
|
| 15 |
|
| Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka. |
|
| 16 |
|
| Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni |
|
| 17 |
|
| sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama. |
|
| 18 |
|
| Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka. |
|
| 19 |
|
| Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya! |
|
| 20 |
|
| Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai. |
|
| 21 |
|
| Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi, |
|
| 22 |
|
| na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka. |
|
| 23 |
|
| Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana. |
|
| 24 |
|
| Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. |
|
| 25 |
|
| Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai. |
|
| 26 |
|
| Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada. |
|
| 27 |
|
| Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci. |
|
| 28 |
|
| Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka. |
|
|
|
|