|
| 1 |
|
| Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka? |
|
| 2 |
|
| Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna. |
|
| 3 |
|
| Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki. |
|
| 4 |
|
| Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu. |
|
| 5 |
|
| Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi. |
|
| 6 |
|
| Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu. |
|
| 7 |
|
| Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka. |
|
| 8 |
|
| Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar. |
|
| 9 |
|
| Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba. |
|
| 10 |
|
| Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne? |
|
| 11 |
|
| Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su! |
|
| 12 |
|
| Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya. |
|
| 13 |
|
| Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye. |
|
| 14 |
|
| Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada. |
|
| 15 |
|
| Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa. |
|
| 16 |
|
| Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata. |
|
| 17 |
|
| Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina. |
|
| 18 |
|
| Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka. |
|
| 19 |
|
| Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba. |
|
| 20 |
|
| Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar. |
|
| 21 |
|
| Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka. |
|
| 22 |
|
| Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini. |
|
| 23 |
|
| Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi. |
|
|
|
|