Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Allah sananne ne a Yahuza, Mashahuri ne kuma a Isra'ila. |
| 2 |
| Wurin zamansa yana Urushalima, A dutsen Sihiyona zatinsa yake. |
| 3 |
| A can yake kakkarya kiban abokan gāba, Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu. |
| 4 |
| Ina misalin darajarka, ya Allah! Ina misalin ɗaukakarka a sa'ad da ka komo daga kan duwatsu, Daga korar abokan gābanka! |
| 5 |
| An kwashe ganimar sojojinsu masu ƙarfin hali, Yanzu suna barci, barcin matattu, Ba waninsu da ya ragu, Da zai yi amfani da makamansa. |
| 6 |
| Sa'ad da ka fafare su, ya Allah na Yakubu, Dawakansu da mahayansu suka fāɗi matattu. |
| 7 |
| Amma mutane suna jin tsoronka! Wa zai iya tsayawa a gabanka Sa'ad da ka yi fushi? |
| 8 |
| Daga Sama ka sanar da shari'arka, Duniya ta tsorata, ta yi tsit, |
| 9 |
| Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci, Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya. |
| 10 |
| Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka. |
| 11 |
| Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa, Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai. Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa, |
| 12 |
| Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai, Ya tsoratar da manyan sarakuna. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/076.mp3
150
76