Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni. |
| 2 |
| Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu. |
| 3 |
| Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. |
| 4 |
| ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana. |
| 5 |
| Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa; |
| 6 |
| na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani. |
| 7 |
| “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba? |
| 8 |
| Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci? |
| 9 |
| Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” |
| 10 |
| Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.” |
| 11 |
| Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā. |
| 12 |
| Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata. |
| 13 |
| Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu? |
| 14 |
| Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane. |
| 15 |
| Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. |
| 16 |
| Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza. |
| 17 |
| Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya. |
| 18 |
| Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza. |
| 19 |
| Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba. |
| 20 |
| Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/077.mp3
150
77