Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai. |
| 2 |
| Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya. |
| 3 |
| Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu. |
| 4 |
| Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. |
| 5 |
| Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta? |
| 6 |
| Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka; |
| 7 |
| gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa. |
| 8 |
| Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai. |
| 9 |
| Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka. |
| 10 |
| Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar. |
| 11 |
| Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa. |
| 12 |
| Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji. |
| 13 |
| Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/079.mp3
150
79