Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya. Yabonka ya kai har sammai, |
| 2 |
| Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka. |
| 3 |
| Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi, Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu, |
| 4 |
| Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi, Mutum kurum, har da kake lura da shi? |
| 5 |
| Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi, Ka naɗa shi da daraja da girma! |
| 6 |
| Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta, Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa, |
| 7 |
| Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji, |
| 8 |
| Da tsuntsaye da kifaye, Da dukan halittar da suke cikin tekuna. |
| 9 |
| Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/008.mp3
150
8