Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai. |
| 2 |
| Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru. |
| 3 |
| Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu, |
| 4 |
| wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi? |
| 5 |
| Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma. |
| 6 |
| Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa, |
| 7 |
| dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji, |
| 8 |
| tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku. |
| 9 |
| Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/008.mp3
150
8