Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka |
| 2 |
| a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu. |
| 3 |
| Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. |
| 4 |
| Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka? |
| 5 |
| Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf. |
| 6 |
| Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a. |
| 7 |
| Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu. |
| 8 |
| Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi. |
| 9 |
| Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa. |
| 10 |
| Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa. |
| 11 |
| Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi. |
| 12 |
| Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa? |
| 13 |
| Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa. |
| 14 |
| Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi, |
| 15 |
| saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka. |
| 16 |
| An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka. |
| 17 |
| Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka. |
| 18 |
| Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka. |
| 19 |
| Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/080.mp3
150
80