Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu, Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu! |
| 2 |
| A fara waƙa, ku buga bandiri, Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu. |
| 3 |
| Ku busa ƙaho domin idin, A amaryar wata, Da a tsakiyar farin wata. |
| 4 |
| Wannan doka ce a Isra'ila, Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu. |
| 5 |
| Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila, A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar. Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa, |
| 6 |
| “Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā, Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku. |
| 7 |
| Sa'ad da kuke shan wahala Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku. Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku, Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba. |
| 8 |
| “Ya kuma jama'ata Isra'ila ku kasa kunne, Ina kuwa so ku saurara gare ni. |
| 9 |
| Faufau kada ku bauta wa gumaka, Ko ku yi sujada ga wanina. |
| 10 |
| Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku. |
| 11 |
| “Amma jama'ata ba su kasa kunne gare ni ba. Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya. |
| 12 |
| Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu, Su aikata duk irin abin da suka ga dama. |
| 13 |
| Ina kuwa so jama'ata su kasa kunne gare ni, Su kuwa yi mini biyayya! |
| 14 |
| Da sai in kori abokan gābansu nan da nan, In yi nasara da dukan maƙiyansu. |
| 15 |
| Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro, Hukuncinsu na har abada ne. |
| 16 |
| Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama, In ƙosar da ku da zuma.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/081.mp3
150
81