Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Allah, kada ka yi shiru, Kada ka tsaya cik, Ya Allah, kada kuma ka yi tsit! |
| 2 |
| Duba, abokan gābanka suna tawaye, Maƙiyanka sun tayar. |
| 3 |
| Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama'arka, Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu. |
| 4 |
| Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al'ummarsu, Don a manta da Isra'ila har abada!” |
| 5 |
| Suka yarda a kan abin da suka shirya, Suka haɗa kai gāba da kai. |
| 6 |
| Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa, Da mutanen Mowab, da Hagarawa, |
| 7 |
| Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek, Da na Filistiya, da na Taya. |
| 8 |
| Assuriya ma ta haɗa kai da su, Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu. |
| 9 |
| Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa, Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera Da Yabin a Kogin Kishon, |
| 10 |
| Waɗanda aka kora a Endor, Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa. |
| 11 |
| Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib, Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna, |
| 12 |
| Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.” |
| 13 |
| Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura, Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa. |
| 14 |
| Kamar yadda wuta take cin jeji, Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai, |
| 15 |
| Ka runtume su da hadirinka, Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi. |
| 16 |
| Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su, Don su so su bauta maka. |
| 17 |
| Ka sa a kore su, a razanar da su har abada, Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci! |
| 18 |
| Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji, Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/083.mp3
150
83