Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi. |
| 2 |
| Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu. |
| 3 |
| Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so. |
| 4 |
| Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.” |
| 5 |
| Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai, |
| 6 |
| tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa, |
| 7 |
| Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya. |
| 8 |
| Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. |
| 9 |
| Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon, |
| 10 |
| waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa. |
| 11 |
| Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna, |
| 12 |
| waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.” |
| 13 |
| Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa, |
| 14 |
| kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu, |
| 15 |
| haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka. |
| 16 |
| Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji. |
| 17 |
| Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci. |
| 18 |
| Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/083.mp3
150
83