Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai, Ya Allah Mai Iko Dukka! |
| 2 |
| A can nake so in kasance! Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji. Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai. |
| 3 |
| Har ba'u ma sukan yi sheƙa, Tsattsewa suna da sheƙunansu, A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu. Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna. |
| 4 |
| Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka, Kullum suna raira yabonka! |
| 5 |
| Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka, Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona. |
| 6 |
| Sa'ad da suke ratsa busasshen kwari, Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa, Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna. |
| 7 |
| Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu, Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona! |
| 8 |
| Ka ji addu'ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna, Ka ji ni, ya Allah na Yakubu! |
| 9 |
| Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu, Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka. |
| 10 |
| Kwana guda da za a yi a Haikalinka, Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam. Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna, Da in zauna a gidajen mugaye. |
| 11 |
| Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai. |
| 12 |
| Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka, Ya Allah Mai Runduna! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/084.mp3
150
84