Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki! |
| 2 |
| Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai. |
| 3 |
| Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. |
| 4 |
| Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. |
| 5 |
| Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne. |
| 6 |
| Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna. |
| 7 |
| Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona. |
| 8 |
| Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. |
| 9 |
| Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka. |
| 10 |
| Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye. |
| 11 |
| Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai. |
| 12 |
| Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/084.mp3
150
84