Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub. |
| 2 |
| Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. |
| 3 |
| Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka. |
| 4 |
| Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu. |
| 5 |
| Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki? |
| 6 |
| Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka? |
| 7 |
| Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka. |
| 8 |
| Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta. |
| 9 |
| Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu. |
| 10 |
| Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba. |
| 11 |
| Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama. |
| 12 |
| Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta. |
| 13 |
| Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/085.mp3
150
85