Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma. |
| 2 |
| Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka. |
| 3 |
| Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini. |
| 4 |
| Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina. |
| 5 |
| Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka. |
| 6 |
| Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai. |
| 7 |
| A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini. |
| 8 |
| A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji; babu ayyukan da za a kwatanta da naka. |
| 9 |
| Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka. |
| 10 |
| Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah. |
| 11 |
| Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji, zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka; ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba, don in ji tsoron sunanka. |
| 12 |
| Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada. |
| 13 |
| Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu. |
| 14 |
| Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah; ƙungiyar marasa imani suna neman raina, mutanen da ba su kula da kai ba. |
| 15 |
| Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci. |
| 16 |
| Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai; ka ba wa bawanka ƙarfi; ka ceci ni gama na bauta maka yadda mahaifiyata ta yi. |
| 17 |
| Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/086.mp3
150
86