|
| 1 |
|
| Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai. |
|
| 2 |
|
| Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta. |
|
| 3 |
|
| Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana, |
|
| 4 |
|
| cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” |
|
| 5 |
|
| Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka. |
|
| 6 |
|
| Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya? |
|
| 7 |
|
| Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi. |
|
| 8 |
|
| Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka. |
|
| 9 |
|
| Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su. |
|
| 10 |
|
| Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka. |
|
| 11 |
|
| Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta. |
|
| 12 |
|
| Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka. |
|
| 13 |
|
| Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka. |
|
| 14 |
|
| Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka. |
|
| 15 |
|
| Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji. |
|
| 16 |
|
| Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka. |
|
| 17 |
|
| Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka. |
|
| 18 |
|
| Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce. |
|
| 19 |
|
| Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane. |
|
| 20 |
|
| Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi. |
|
| 21 |
|
| Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi. |
|
| 22 |
|
| Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi. |
|
| 23 |
|
| Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa. |
|
| 24 |
|
| Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi, kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa. |
|
| 25 |
|
| Zan sa hannunsa a bisa teku, hannunsa na dama a bisa koguna. |
|
| 26 |
|
| Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’ |
|
| 27 |
|
| Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya. |
|
| 28 |
|
| Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba. |
|
| 29 |
|
| Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan. |
|
| 30 |
|
| “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba, |
|
| 31 |
|
| in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina, |
|
| 32 |
|
| zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala; |
|
| 33 |
|
| amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba. |
|
| 34 |
|
| Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata. |
|
| 35 |
|
| Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba, |
|
| 36 |
|
| cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana; |
|
| 37 |
|
| zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” |
|
| 38 |
|
| Amma ka ƙi, ka yi ƙyama ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka. |
|
| 39 |
|
| Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura. |
|
| 40 |
|
| Ka rurrushe dukan katangansa ka sa kagaransa suka zama kufai. |
|
| 41 |
|
| Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi; ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa. |
|
| 42 |
|
| Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa; ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki. |
|
| 43 |
|
| Ka juye bakin takobinsa ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba. |
|
| 44 |
|
| Ka kawo ƙarshen darajarsa ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa. |
|
| 45 |
|
| Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa; ka rufe shi da mayafin kunya. |
|
| 46 |
|
| Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta? |
|
| 47 |
|
| Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani! |
|
| 48 |
|
| Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? |
|
| 49 |
|
| Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda? |
|
| 50 |
|
| Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai, |
|
| 51 |
|
| zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka. |
|
| 52 |
|
| Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada! Amin kuma Amin. |
|
|
|
|