|
| 1 |
|
| Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji, Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi. |
|
| 2 |
|
| Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai, Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki! |
|
| 3 |
|
| Magabtana sun jā da baya da suka gan ka, Suka faɗi, suka mutu. |
|
| 4 |
|
| Kai da kake alƙali mai adalci Ka zauna a kursiyinka, Ka kuwa yi shari'ar da ta yi mini daidai. |
|
| 5 |
|
| Ka kā da arna, Ka kuma hallakar da mugaye, Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba. |
|
| 6 |
|
| An hallaka abokan gābanmu har abada, Ka lalatar da biranensu, An kuma manta da su sarai. |
|
| 7 |
|
| Amma Ubangiji sarki ne har abada, Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a. |
|
| 8 |
|
| Yana mulkin duniya da adalci, Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya. |
|
| 9 |
|
| Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, Wurin ɓuya a lokatan wahala. |
|
| 10 |
|
| Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba. |
|
| 11 |
|
| Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona! Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi! |
|
| 12 |
|
| Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya, Ba ya mantawa da kukansu, Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu. |
|
| 13 |
|
| Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini! Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji, |
|
| 14 |
|
| Domin in iya tsayawa a gaban jama'ar Urushalima, In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka. Zan yi farin ciki saboda ka cece ni. |
|
| 15 |
|
| Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki, Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su. |
|
| 16 |
|
| Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci, Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata. |
|
| 17 |
|
| Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye, Da dukan waɗanda suke ƙin Allah. |
|
| 18 |
|
| Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba, Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada. |
|
| 19 |
|
| Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka! Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su. |
|
| 20 |
|
| Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji, Ka sa su sani su mutane ne kawai. |
|
|
|
|