|
| 1 |
|
| Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka. |
|
| 2 |
|
| Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka. |
|
| 3 |
|
| Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka. |
|
| 4 |
|
| Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci. |
|
| 5 |
|
| Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin. |
|
| 6 |
|
| Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu. |
|
| 7 |
|
| Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a. |
|
| 8 |
|
| Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya. |
|
| 9 |
|
| Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala. |
|
| 10 |
|
| Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba. |
|
| 11 |
|
| Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata. |
|
| 12 |
|
| Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala. |
|
| 13 |
|
| Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa, |
|
| 14 |
|
| don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka. |
|
| 15 |
|
| Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye. |
|
| 16 |
|
| An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. |
|
| 17 |
|
| Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. |
|
| 18 |
|
| Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka. |
|
| 19 |
|
| Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka. |
|
| 20 |
|
| Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. |
|
|
|
|