Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai. |
| 2 |
| Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne. |
| 3 |
| Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.” |
| 4 |
| Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare. |
| 5 |
| Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya, |
| 6 |
| ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane. |
| 7 |
| An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka. |
| 8 |
| Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka. |
| 9 |
| Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi. |
| 10 |
| Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare. |
| 11 |
| Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai. |
| 12 |
| Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima. |
| 13 |
| Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka. |
| 14 |
| Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu. |
| 15 |
| Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala. |
| 16 |
| Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga ’ya’yansu. |
| 17 |
| Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/090.mp3
150
90