Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki. |
| 2 |
| Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.” |
| 3 |
| Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa. |
| 4 |
| Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga. |
| 5 |
| Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba, |
| 6 |
| ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana. |
| 7 |
| Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai. |
| 8 |
| Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye. |
| 9 |
| In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata, |
| 10 |
| to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka. |
| 11 |
| Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka; |
| 12 |
| za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse. |
| 13 |
| Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji. |
| 14 |
| Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana. |
| 15 |
| Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi. |
| 16 |
| Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/091.mp3
150
91