Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya, A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka, |
| 2 |
| A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya, Amincinka kuma kowane maraice, |
| 3 |
| Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya, Da amon garaya mai daɗi. |
| 4 |
| Ya Ubangiji, Ayyukanka masu iko suna sa ni murna, Saboda abin da ka aikata Ina raira waƙa domin farin ciki. |
| 5 |
| Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji! Tunaninka da zurfi suke! |
| 6 |
| Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba, Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba, |
| 7 |
| Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, Duk da haka za a hallaka su ɗungum. |
| 8 |
| Gama kai, ya Ubangiji, Maɗaukaki ne har abada. |
| 9 |
| Mun sani maƙiyanka za su mutu, Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su. |
| 10 |
| Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa, Ka sa mini albarka da farin ciki. |
| 11 |
| Na ga fāɗuwar maƙiyana, Na ji kukan mugaye. |
| 12 |
| Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon. |
| 13 |
| Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji, Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu. |
| 14 |
| Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu, A kullum kuwa kore shar suke, Suna da ƙarfinsu kuma. |
| 15 |
| Wannan ya nuna Ubangiji adali ne, Shi wanda yake kāre ni, Ba kuskure a gare shi. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/092.mp3
150
92