Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, |
| 2 |
| don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare, |
| 3 |
| da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya. |
| 4 |
| Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. |
| 5 |
| Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai! |
| 6 |
| Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba, |
| 7 |
| cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada. |
| 8 |
| Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada. |
| 9 |
| Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta. |
| 10 |
| Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina. |
| 11 |
| Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana. |
| 12 |
| Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon; |
| 13 |
| da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. |
| 14 |
| Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar, |
| 15 |
| suna shela cewa, “ Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/092.mp3
150
92