Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci, Ka bayyana fushinka! |
| 2 |
| Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a, Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai Abin da ya dace da su! |
| 3 |
| Har yaushe mugaye za su yi ta murna? Har yaushe ne, ya Ubangiji? |
| 4 |
| Har yaushe za su yi shakiyanci, Su yi ta ɗaga kai? Har yaushe, ya Ubangiji? |
| 5 |
| Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji, Suna zaluntar waɗanda suke naka. |
| 6 |
| Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu. |
| 7 |
| Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu, Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!” |
| 8 |
| Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka? Sai yaushe za ku koya? |
| 9 |
| Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba? Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba? |
| 10 |
| Shi ne yake shugabancin sauran al'umma, ba zai hukunta su ba? Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne? |
| 11 |
| Ubangiji ya san tunaninsu, Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali. |
| 12 |
| Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa, Mutumin da kake koya masa shari'arka. |
| 13 |
| Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala, Kafin a haƙa wa mugaye kabari. |
| 14 |
| Ubangiji ba zai rabu da jama'arsa ba, Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba. |
| 15 |
| Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai, Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi. |
| 16 |
| Wa zai tsaya mini gāba da mugaye? Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta? |
| 17 |
| Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba, Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi. |
| 18 |
| Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni. |
| 19 |
| Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa, Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna. |
| 20 |
| Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya, Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu, |
| 21 |
| Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya, Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa. |
| 22 |
| Amma Ubangiji yakan kāre ni, Allahna yakan kiyaye ni. |
| 23 |
| Shi zai hukunta su saboda muguntarsu, Ya hallaka su saboda zunubansu. Ubangiji Allahnmu zai hallaka su. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/094.mp3
150
94