Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. |
| 2 |
| Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. |
| 3 |
| Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli. |
| 4 |
| A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. |
| 5 |
| Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. |
| 6 |
| Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu; |
| 7 |
| gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa, |
| 8 |
| “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada, |
| 9 |
| inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi. |
| 10 |
| Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’ |
| 11 |
| Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/095.mp3
150
95