Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji! Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka! |
| 2 |
| Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi! Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa, “Ya cece mu!” |
| 3 |
| Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma, Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai. |
| 4 |
| Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi, Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli. |
| 5 |
| Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai, Amma Ubangiji ne ya yi sammai. |
| 6 |
| Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi, Girma da jamali suna cikin Haikalinsa. |
| 7 |
| Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji! Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa! |
| 8 |
| Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka, Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa. |
| 9 |
| Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana, Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka! |
| 10 |
| A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne! Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta, Ba za a iya kaushe ta ba, Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.” |
| 11 |
| Duniya da sararin sama, ku yi murna! Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki, |
| 12 |
| Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku! Sa'an nan itatuwan da suke cikin kurama Za su ta da murya saboda farin ciki |
| 13 |
| A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya. Zai mallaki dukan jama'ar duniya Da adalci da gaskiya. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/096.mp3
150
96