Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. |
| 2 |
| Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. |
| 3 |
| Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. |
| 4 |
| Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. |
| 5 |
| Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. |
| 6 |
| Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa. |
| 7 |
| Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. |
| 8 |
| Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. |
| 9 |
| Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. |
| 10 |
| Ku faɗa cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya. |
| 11 |
| Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa; |
| 12 |
| bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki; |
| 13 |
| za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/096.mp3
150
96