Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya! Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna! |
| 2 |
| Gajimare da duhu sun kewaye shi. A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa. |
| 3 |
| Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa Waɗanda suke kewaye da shi. |
| 4 |
| Walƙiyarsa ta haskaka duniya, Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki. |
| 5 |
| Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma, A gaban Ubangijin dukan duniya. |
| 6 |
| Sammai suna shelar adalcinsa, Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa. |
| 7 |
| Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya, Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu. Dukan alloli za su rusuna a gabansa. |
| 8 |
| Jama'ar Sihiyona suna murna, Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki, Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji! |
| 9 |
| Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya, Ka fi sauran alloli duka girma. |
| 10 |
| Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta. Yakan kiyaye rayukan jama'arsa, Yakan cece su daga ikon mugaye. |
| 11 |
| Haske yakan haskaka adalai, Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta. |
| 12 |
| Dukanku adalai ku yi murna, Saboda abin da Ubangiji ya yi! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi, Ku yi masa godiya! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/097.mp3
150
97