Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki. |
| 2 |
| Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa. |
| 3 |
| Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe. |
| 4 |
| Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki. |
| 5 |
| Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya. |
| 6 |
| Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa. |
| 7 |
| Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli! |
| 8 |
| Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji. |
| 9 |
| Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli. |
| 10 |
| Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye. |
| 11 |
| An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya. |
| 12 |
| Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/097.mp3
150
97