Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. |
| 2 |
| Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. |
| 3 |
| Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. |
| 4 |
| Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi; |
| 5 |
| ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa, |
| 6 |
| tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki. |
| 7 |
| Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. |
| 8 |
| Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; |
| 9 |
| bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/098.mp3
150
98