Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza. |
| 2 |
| Ubangiji mai iko ne a Sihiyona, Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma. |
| 3 |
| Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki, Mai Tsarki ne shi! |
| 4 |
| Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai, Ka kawo adalci cikin Isra'ila, Ka kawo adalci da gaskiya. |
| 5 |
| Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a gaban kursiyinsa! Mai Tsarki ne shi! |
| 6 |
| Musa da Haruna firistocinsa ne, Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne. Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu. |
| 7 |
| Ya yi magana da su daga girgije, Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su. |
| 8 |
| Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka, Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara, Amma kakan hukunta su saboda zunubansu. |
| 9 |
| Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki! Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/099.mp3
150
99