Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza. |
| 2 |
| Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai. |
| 3 |
| Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne. |
| 4 |
| Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai. |
| 5 |
| Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne. |
| 6 |
| Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu. |
| 7 |
| Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su. |
| 8 |
| Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau. |
| 9 |
| Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/099.mp3
150
99