|
| 1 |
|
| Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka, |
|
| 2 |
|
| kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi, |
|
| 3 |
|
| in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa, |
|
| 4 |
|
| in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya, |
|
| 5 |
|
| to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah. |
|
| 6 |
|
| Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito. |
|
| 7 |
|
| Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi, |
|
| 8 |
|
| gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa. |
|
| 9 |
|
| Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau. |
|
| 10 |
|
| Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai. |
|
| 11 |
|
| Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora. |
|
| 12 |
|
| Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci, |
|
| 13 |
|
| waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu, |
|
| 14 |
|
| waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci, |
|
| 15 |
|
| waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu. |
|
| 16 |
|
| Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta, |
|
| 17 |
|
| wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah. |
|
| 18 |
|
| Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu. |
|
| 19 |
|
| Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai. |
|
| 20 |
|
| Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai. |
|
| 21 |
|
| Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta; |
|
| 22 |
|
| amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta. |
|
|
|
|