|
| 1 |
|
| Ɗana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na faɗa maka ka yi. |
|
| 2 |
|
| Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata. |
|
| 3 |
|
| Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka. |
|
| 4 |
|
| Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin hulɗar da kake yi da mutane. |
|
| 5 |
|
| Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. |
|
| 6 |
|
| A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai. |
|
| 7 |
|
| Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta. |
|
| 8 |
|
| Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake sha. |
|
| 9 |
|
| Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka. |
|
| 10 |
|
| Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka. |
|
| 11 |
|
| Ɗana, sa'ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa. |
|
| 12 |
|
| Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi. |
|
| 13 |
|
| Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi. |
|
| 14 |
|
| Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya. |
|
| 15 |
|
| Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani. |
|
| 16 |
|
| Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja. |
|
| 17 |
|
| Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka. |
|
| 18 |
|
| Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da 'ya'ya. |
|
| 19 |
|
| Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa, Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa. |
|
| 20 |
|
| Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu, Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya. |
|
| 21 |
|
| Ɗana ka riƙe hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai. |
|
| 22 |
|
| Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki. |
|
| 23 |
|
| Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe. |
|
| 24 |
|
| Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare. |
|
| 25 |
|
| Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri. |
|
| 26 |
|
| Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba. |
|
| 27 |
|
| Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa. |
|
| 28 |
|
| Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu. |
|
| 29 |
|
| Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai. |
|
| 30 |
|
| Kada ka yi jayayya ba dalili da wanda bai taɓa cutarka ba. |
|
| 31 |
|
| Kada ka ji kishin masu ta da zaune tsaye, ko ka yi sha'awar aikata ayyukansu, |
|
| 32 |
|
| gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su. |
|
| 33 |
|
| Ubangiji yakan la'antar da gidajen masu mugunta, amma yakan sa wa gidajen adalai albarka. |
|
| 34 |
|
| Ba ruwansa da masu girmankai, amma masu tawali'u sukan sami tagomashi a wurinsa. |
|
| 35 |
|
| Mutane masu hikima za su sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya. |
|
|
|
|