|
| 1 |
|
| Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka, |
|
| 2 |
|
| gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata. |
|
| 3 |
|
| Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka. |
|
| 4 |
|
| Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane. |
|
| 5 |
|
| Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; |
|
| 6 |
|
| cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe. |
|
| 7 |
|
| Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta. |
|
| 8 |
|
| Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka. |
|
| 9 |
|
| Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; |
|
| 10 |
|
| ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi. |
|
| 11 |
|
| Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa, |
|
| 12 |
|
| domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi. |
|
| 13 |
|
| Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi, |
|
| 14 |
|
| gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya. |
|
| 15 |
|
| Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita. |
|
| 16 |
|
| Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma. |
|
| 17 |
|
| Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne. |
|
| 18 |
|
| Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka. |
|
| 19 |
|
| Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke; |
|
| 20 |
|
| ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa. |
|
| 21 |
|
| Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai; |
|
| 22 |
|
| za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka. |
|
| 23 |
|
| Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba; |
|
| 24 |
|
| sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi. |
|
| 25 |
|
| Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye, |
|
| 26 |
|
| gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko. |
|
| 27 |
|
| Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka. |
|
| 28 |
|
| Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu. |
|
| 29 |
|
| Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai. |
|
| 30 |
|
| Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba. |
|
| 31 |
|
| Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu. |
|
| 32 |
|
| Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi. |
|
| 33 |
|
| La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali. |
|
| 34 |
|
| Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri. |
|
| 35 |
|
| Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya. |
|
|
|
|