|
| 1 |
|
| 'Ya'yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai. |
|
| 2 |
|
| Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka. |
|
| 3 |
|
| Sa'ad da nake ɗan yaro tilo a wurin iyayena, |
|
| 4 |
|
| mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu. |
|
| 5 |
|
| Ka nemi hikima da basira! Kada ka manta ko ka ƙyale abin da na faɗa. |
|
| 6 |
|
| Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka. |
|
| 7 |
|
| Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira. |
|
| 8 |
|
| Ka ƙaunaci hikima, za ta girmama ka. Ka rungume ta, za ta kawo maka daraja. |
|
| 9 |
|
| Za ta zamar maka rawanin daraja.” |
|
| 10 |
|
| Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai. |
|
| 11 |
|
| Gama na koya maka hikima da hanyar zama mai kyau. |
|
| 12 |
|
| Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa'ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba. |
|
| 13 |
|
| Kullum ka tuna da abin da ka koya, iliminka shi ne ranka, ka lura da shi da kyau. |
|
| 14 |
|
| Kada ka tafi inda mugaye suke tafiya, kada ka bi gurbin mugaye. |
|
| 15 |
|
| Kada ka yi mugunta! Ka nisance ta! Ka ƙi ta, yi tafiyarka. |
|
| 16 |
|
| Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani. |
|
| 17 |
|
| Mugunta da ta'adi kamar ci da sha suke a gare su. |
|
| 18 |
|
| Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka. |
|
| 19 |
|
| Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba. |
|
| 20 |
|
| Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa. Ka kasa kunne ga kalmomina. |
|
| 21 |
|
| Kada ka kuskura su rabu da kai, ka tuna da su, ka ƙaunace su. |
|
| 22 |
|
| Za su ba da rai da lafiya ga dukan wanda ya fahimce su. |
|
| 23 |
|
| Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja. |
|
| 24 |
|
| Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗawa. |
|
| 25 |
|
| Ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro. |
|
| 26 |
|
| Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai. |
|
| 27 |
|
| Ka rabu da mugunta ka yi tafiyarka sosai, kada ka kauce ko da taki ɗaya daga hanyar da take daidai. |
|
|
|
|