|
| 1 |
|
| Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi. |
|
| 2 |
|
| Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata. |
|
| 3 |
|
| Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata, |
|
| 4 |
|
| ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu. |
|
| 5 |
|
| Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su. |
|
| 6 |
|
| Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai. |
|
| 7 |
|
| Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi. |
|
| 8 |
|
| Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka. |
|
| 9 |
|
| Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.” |
|
| 10 |
|
| Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa. |
|
| 11 |
|
| Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi. |
|
| 12 |
|
| Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba. |
|
| 13 |
|
| Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne. |
|
| 14 |
|
| Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye. |
|
| 15 |
|
| Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka. |
|
| 16 |
|
| Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani. |
|
| 17 |
|
| Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su. |
|
| 18 |
|
| Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka. |
|
| 19 |
|
| Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe. |
|
| 20 |
|
| Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina. |
|
| 21 |
|
| Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka; |
|
| 22 |
|
| gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum. |
|
| 23 |
|
| Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne. |
|
| 24 |
|
| Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka. |
|
| 25 |
|
| Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka. |
|
| 26 |
|
| Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai. |
|
| 27 |
|
| Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta. |
|
|
: |
| 1 | | 2 | | 3 | | 4 | | 5 | | 6 | | 7 | | 8 | | 9 | | 10 | | 11 | | 12 | | 13 | | 14 | | 15 | | 16 | | 17 | | 18 | | 19 | | 20 | | 21 | | 22 | | 23 | | 24 | | 25 | | 26 | | 27 | 1
1
1 |
|
|---|
|
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/proverbs/004.mp3
31
4