Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ɗana, ka mai da hankali, ka kasa kunne ga hikimata da basirata. |
| 2 |
| Sa'an nan ne za ka san yadda za ka yi kome daidai, kalmominka za su nuna kana da ilimi. |
| 3 |
| Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi. |
| 4 |
| Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba. |
| 5 |
| Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce. |
| 6 |
| Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba. |
| 7 |
| 'Ya'yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa. |
| 8 |
| Ku yi nesa da irin wannan mace! Kada ku yarda ku yi ko kusa da ƙofarta! |
| 9 |
| Idan kuwa kun yi, girmamawar da ake yi muku za ta zama ta waɗansu. Za ku yi mutuwar ƙuruciya ta hannun mutane marasa imani. |
| 10 |
| Hakika, baƙi za su kwashe dukan dukiyarku, abin da kuka sha wahalar samu kuma zai zama rabon wani dabam. |
| 11 |
| Za ku kwanta kuna nishi a kan gadon mutuwa, namanku da tsokokinku za su zagwanye. |
| 12 |
| Sa'an nan za ku ce, “Me ya sa ban taɓa koyo ba? Me ya sa ban yarda wani ya kwaɓe ni ba? |
| 13 |
| Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba. |
| 14 |
| Farat ɗaya sai aka kunyatar da ni a bainar jama'a.” |
| 15 |
| Ka yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta ita kaɗai. |
| 16 |
| Idan kuma waɗansu mata sun haifa maka 'ya'ya, 'ya'yan nan ba za su yi maka wani amfani ba. |
| 17 |
| 'Ya'yanka za su yi girma su taimake ka, ba na baƙi ba. |
| 18 |
| Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro, |
| 19 |
| kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa. Bari kyanta ya ɗau hankalinka. Bari ƙaunarta ta kewaye ka. |
| 20 |
| Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta? |
| 21 |
| Ubangiji yana ganin dukan abin da kake yi. Inda ka shiga duk yana kallonka. |
| 22 |
| Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi. |
| 23 |
| Yakan mutu saboda rashin kamewarsa, cikakkiyar wautarsa za ta kai shi kabarinsa. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/proverbs/005.mp3
31
5