Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ku kasa kunne! Hikima tana kira. Tana so a ji ta. |
| 2 |
| Tana tsaye bisa kan tuddai a bakin hanya Da a mararraban hanyoyi. |
| 3 |
| A ƙofofin shiga birni, tana kira, |
| 4 |
| “Ina roƙonku, ya ku, 'yan adam, Ina kiran kowane mutum da yake a duniya. |
| 5 |
| Ba ku balaga ba? To, ku balaga. Ku wawaye ne? Ku koyi hankali. |
| 6 |
| Ku kasa kunne ga jawabina mafi kyau, Dukan abin da na faɗa muku daidai ne. |
| 7 |
| Abin da na faɗa gaskiya ne, Ƙarairayi abin ƙi ne a gare ni. |
| 8 |
| Kowane abu da na faɗa gaskiya ne, Ba wani abu da yake na laifi ko na ruɗawa. |
| 9 |
| Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari, Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe. |
| 10 |
| Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa, Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa. |
| 11 |
| “Ni ce hikima, na fi lu'ulu'ai, Cikin dukan abin da kake so, ba kamata. |
| 12 |
| Ni ce hikima, ina da basira, Ina da ilimi da faɗar daidai. |
| 13 |
| Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji, Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi, Da maganganu na ƙarya. |
| 14 |
| Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi. Ina da fahimi, ina da ƙarfi. |
| 15 |
| Nakan taimaki sarakuna su yi mulki, Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau. |
| 16 |
| Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki, Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya. |
| 17 |
| Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni. |
| 18 |
| Ina da dukiya da daraja da zan bayar, Da wadata da nasara kuma. |
| 19 |
| Abin da za ka samu daga gare ni Ya fi zinariya kyau, da azurfa tsantsa. |
| 20 |
| A kan hanyar adalci nake tafiya, Rankai a kan hanyoyin gaskiya. |
| 21 |
| Ina ba da dukiya ga waɗanda suke ƙaunata, Ina kuma cika gidajensu da wadata. |
| 22 |
| “Ni ce halittar farko da Ubangiji Ya fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni. |
| 23 |
| Da farkon farawa ni aka fara halittawa Kafin a yi duniya. |
| 24 |
| Ni aka fara yi kafin tekuna, A sa'ad da ba maɓuɓɓugan ruwa. |
| 25 |
| Ni aka fara yi kafin a yi duwatsu, Kafin a kafa tuddai a wurarensu, |
| 26 |
| Kafin Allah ya halicci duniya da filayenta, Ko ɗan ɓarɓashin ƙasa. |
| 27 |
| A can nake sa'ad da ya shata sararin sama, Da sa'ad da ya shimfiɗa al'arshi a hayin tekuna, |
| 28 |
| Da sa'ad da ya sa gizagizai a sararin sama, Ya buɗe maɓuɓɓugan teku, |
| 29 |
| Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa. Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya. |
| 30 |
| Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini, Ni ce abar murnarsa kowace rana, A ko yaushe ina farin ciki a gabansa. |
| 31 |
| Ina farin ciki da duniya, Ina murna da 'yan adam. |
| 32 |
| “Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni, Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki. |
| 33 |
| Ku saurari abin da aka koya muku, Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita. |
| 34 |
| Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki haka nan, Wato yakan tsaya a ƙofata ko yaushe, Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana. |
| 35 |
| Mutumin da ya same ni ya sami rai, Ubangiji zai ji daɗinsa. |
| 36 |
| Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa, Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/proverbs/008.mp3
31
8