Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa. |
| 2 |
| Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye. |
| 3 |
| Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa. |
| 4 |
| Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus. |
| 5 |
| Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki. |
| 6 |
| Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo! |
| 7 |
| Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace. |
| 8 |
| Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama ’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa, |
| 9 |
| kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora. |
| 10 |
| Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne. |
| 11 |
| Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye. |
| 12 |
| Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata. |
| 13 |
| Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/songofsolomon/007.mp3
8
7