|
| 1 |
|
| Ni ne mutumin da ya sha wuyar horon Ubangiji. |
|
| 2 |
|
| Ya kore ni zuwa cikin duhu baƙi ƙirin. |
|
| 3 |
|
| Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini. |
|
| 4 |
|
| Ya sa naman jikina da fatar jikina su lalace, Ya kuma kakkarya ƙasusuwana. |
|
| 5 |
|
| Ya kewaye ni da yaƙi, Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala. |
|
| 6 |
|
| Ya zaunar da ni cikin duhu, Kamar waɗanda suka daɗe da mutuwa. |
|
| 7 |
|
| Ya kewaye ni da garu don kada in tsere, Ya ɗaure ni da sarƙa mai nauyi. |
|
| 8 |
|
| Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako, Ya yi watsi da addu'ata. |
|
| 9 |
|
| Ya toshe hanyata da sassaƙaƙƙun duwatsu, Ya karkatar da hanyoyina. |
|
| 10 |
|
| Ya zamar mini kamar beyar wanda yake fako, Kamar zaki a ɓoye cikin ruƙuƙi. |
|
| 11 |
|
| Ya bauɗar da ni daga hanyata, ya yayyage ni, Ya maishe ni, ba ni a kowa. |
|
| 12 |
|
| Ya ja bakansa, ya sa in zama abin baratarsa. |
|
| 13 |
|
| Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa. |
|
| 14 |
|
| Na zama abin dariya ga dukan mutane, Dukan yini suna yi mini waƙar zambo. |
|
| 15 |
|
| Ya shayar da ni da ruwan ɗaci, Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci. |
|
| 16 |
|
| Ya sa in tauna tsakuwa da haƙorana, Ya zaunar da ni cikin ƙura. |
|
| 17 |
|
| An raba ni da salama, Na manta da abar da ake ce da ita wadata. |
|
| 18 |
|
| Sai na ce, “Darajata ta ƙare, Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.” |
|
| 19 |
|
| Ka tuna da azabata, da galabaitata, Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi. |
|
| 20 |
|
| Kullum raina yana tunanin azabaina, Raina kuwa ya karai. |
|
| 21 |
|
| Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba. |
|
| 22 |
|
| Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. |
|
| 23 |
|
| Su sababbi ne kowace safiya, Amincinka kuma mai girma ne. |
|
| 24 |
|
| Na ce, “Ubangiji shi ne nawa, Saboda haka zan sa zuciya gare shi.” |
|
| 25 |
|
| Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa, Da wanda suke nemansa kuma. |
|
| 26 |
|
| Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa, |
|
| 27 |
|
| Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro. |
|
| 28 |
|
| Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiru Sa'ad da yake da damuwa. |
|
| 29 |
|
| Bari ya kwanta cikin ƙura, Watakila akwai sauran sa zuciya. |
|
| 30 |
|
| Bari ya yarda a mari kumatunsa, Ya haƙura da cin mutunci. |
|
| 31 |
|
| Gama Ubangiji ba zai yashe mu har abada ba. |
|
| 32 |
|
| Ko da ya sa ɓacin rai, Zai ji tausayi kuma, Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa. |
|
| 33 |
|
| Gama ba da gangan ba ne yakan wahalar da 'yan adam Ko ya sa su baƙin ciki. |
|
| 34 |
|
| Ubangiji bai yarda a danne 'Yan kurkuku na duniya ba. |
|
| 35 |
|
| Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsa A gaban Maɗaukaki ba, |
|
| 36 |
|
| Ko kuwa a karkatar wa mutum da shari'arsa. |
|
| 37 |
|
| Wa ya umarta, abin kuwa ya faru, In ba Ubangiji ne ya umarta ba? |
|
| 38 |
|
| Ba daga bakin Maɗaukaki Alheri da mugunta suke fitowa ne ba? |
|
| 39 |
|
| Don me ɗan adam Zai yi gunaguni a kan hukuncin zunubansa? |
|
| 40 |
|
| Bari mu jarraba, mu bincika hanyoyinmu, Sa'an nan mu komo wurin Ubangiji. |
|
| 41 |
|
| Bari mu roƙi Allah na Sama, Muna miƙa hannuwanmu sama, mu ce, |
|
| 42 |
|
| “Mun yi zunubi, mun tayar, Kai kuwa ba ka gafarta ba. |
|
| 43 |
|
| “Ka yafa fushi, ka runtume mu, Kana karkashe mu ba tausayi. |
|
| 44 |
|
| Ka kuma rufe kanka da gajimare Don kada addu'a ta kai wurinka. |
|
| 45 |
|
| Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane. |
|
| 46 |
|
| “Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a. |
|
| 47 |
|
| Tsoro, da wushefe, Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana. |
|
| 48 |
|
| Hawaye suna gangarawa daga idanuna kamar ruwan koguna, Saboda an hallaka mutanena. |
|
| 49 |
|
| “Hawayena suna ta gangarawa, ba tsayawa, ba hutawa, |
|
| 50 |
|
| Har lokacin da Ubangiji daga Sama ya duba, ya gani. |
|
| 51 |
|
| Ganin azabar 'yan matan birnina Ya sa ni baƙin ciki. |
|
| 52 |
|
| “Waɗanda suke maƙiyana ba dalili Sun farauce ni kamar tsuntsu. |
|
| 53 |
|
| Sun jefa ni da rai a cikin rami, Suka rufe ni da duwatsu. |
|
| 54 |
|
| Ruwa ya sha kaina, Sai na ce, ‘Na halaka.’ |
|
| 55 |
|
| “Ya Ubangiji, na yi kira ga sunanka Daga cikin rami mai zurfi. |
|
| 56 |
|
| Ka kuwa ji muryata. Kada ka rufe kunnenka ga jin kukana na neman taimako. |
|
| 57 |
|
| Sa'ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa. Sa'an nan ka ce mini kada in ji tsoro. |
|
| 58 |
|
| “Ka karɓi da'awata, ya Ubangiji, Ka kuwa fanshi raina. |
|
| 59 |
|
| Ka ga laifin da aka yi mini, Sai ka shara'anta da'awata, ya Ubangiji. |
|
| 60 |
|
| Ka ga dukan irin sakayyarsu, Da dukan dabarun da suke yi mini. |
|
| 61 |
|
| “Ya Ubangiji, ka ji zargi Da dukan dabarun da suke yi mini. |
|
| 62 |
|
| Leɓunan maƙiyana da tunaninsu Suna gāba da ni dukan yini. |
|
| 63 |
|
| Suna raira mini waƙar zambo sa'ad da suke zaune, Da lokacin da suka tashi. |
|
| 64 |
|
| “Ya Ubangiji, za ka sāka musu bisa ga ayyukansu, |
|
| 65 |
|
| Za ka ba su tattaurar zuciya, La'anarka kuwa za ta zauna a kansu! |
|
| 66 |
|
| Da fushi za ka runtume su Har ka hallaka su a duniya, ya Ubangiji!” |
|
|
|
|