|
| 1 |
|
| Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji. |
|
| 2 |
|
| Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske; |
|
| 3 |
|
| ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini. |
|
| 4 |
|
| Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana. |
|
| 5 |
|
| Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala. |
|
| 6 |
|
| Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa. |
|
| 7 |
|
| Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi. |
|
| 8 |
|
| Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata. |
|
| 9 |
|
| Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace. |
|
| 10 |
|
| Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye, |
|
| 11 |
|
| ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako. |
|
| 12 |
|
| Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa. |
|
| 13 |
|
| Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa. |
|
| 14 |
|
| Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini. |
|
| 15 |
|
| Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci. |
|
| 16 |
|
| Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura. |
|
| 17 |
|
| An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata. |
|
| 18 |
|
| Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.” |
|
| 19 |
|
| Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. |
|
| 20 |
|
| Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina. |
|
| 21 |
|
| Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba. |
|
| 22 |
|
| Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. |
|
| 23 |
|
| Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne. |
|
| 24 |
|
| Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.” |
|
| 25 |
|
| Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; |
|
| 26 |
|
| yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji. |
|
| 27 |
|
| Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro. |
|
| 28 |
|
| Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi. |
|
| 29 |
|
| Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege. |
|
| 30 |
|
| Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci. |
|
| 31 |
|
| Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada. |
|
| 32 |
|
| Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa. |
|
| 33 |
|
| Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba. |
|
| 34 |
|
| Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba, |
|
| 35 |
|
| ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki, |
|
| 36 |
|
| ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba? |
|
| 37 |
|
| Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba? |
|
| 38 |
|
| Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba? |
|
| 39 |
|
| Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa? |
|
| 40 |
|
| Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji. |
|
| 41 |
|
| Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce, |
|
| 42 |
|
| “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba. |
|
| 43 |
|
| “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi. |
|
| 44 |
|
| Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka. |
|
| 45 |
|
| Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane. |
|
| 46 |
|
| “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi. |
|
| 47 |
|
| Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.” |
|
| 48 |
|
| Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena. |
|
| 49 |
|
| Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa. |
|
| 50 |
|
| Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani. |
|
| 51 |
|
| Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina. |
|
| 52 |
|
| Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu. |
|
| 53 |
|
| Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu; |
|
| 54 |
|
| ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa. |
|
| 55 |
|
| Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi. |
|
| 56 |
|
| Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.” |
|
| 57 |
|
| Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.” |
|
| 58 |
|
| Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina. |
|
| 59 |
|
| Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya! |
|
| 60 |
|
| Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini. |
|
| 61 |
|
| Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini |
|
| 62 |
|
| Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini. |
|
| 63 |
|
| Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu. |
|
| 64 |
|
| Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi. |
|
| 65 |
|
| Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su. |
|
| 66 |
|
| Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji. |
|
|
|
|