Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha. |
| 2 |
| An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare. |
| 3 |
| Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye. |
| 4 |
| Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace. |
| 5 |
| Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta. |
| 6 |
| Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci. |
| 7 |
| Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu. |
| 8 |
| Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu. |
| 9 |
| Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji. |
| 10 |
| Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa. |
| 11 |
| An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda. |
| 12 |
| An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma. |
| 13 |
| Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace. |
| 14 |
| Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa. |
| 15 |
| Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki. |
| 16 |
| Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi! |
| 17 |
| Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe |
| 18 |
| gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin. |
| 19 |
| Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani. |
| 20 |
| Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa? |
| 21 |
| Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā |
| 22 |
| sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/lamentations/005.mp3
5
5