Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!
Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan. Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim, Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.
An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar, Don ya zama alama. An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.
Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
Dukiyarki, da kayan cinikinki, da hajarki, Da ma'aikatanki da masu ja miki gora, Da masu tattoshe mahaɗan katakanki, Da abokan cinikinki, da dukan sojojinki, Da dukan taron jama'ar da take tare da ke, Sun dulmuya cikin tsakiyar teku a ranar halakarki.